Rahotanni sun nuna cewa zaben na wannan karo na kunshe ne da 'yan takara 5, ciki hadda shugaba mai ci Faure Essozimna Gnassingbe wanda ke neman zarcewa a karo na 3.
An dai fara kada kuri'un ne da karfe 7 na safiyar ranar ta Asabar, aka kuma kammala da karfe 4 na yamma. Haka kuma masu sa ido sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Bayan kada kuri'un an kuma fara kididdiga kamar dai yadda aka tsara tun da farko.
Kimanin masu aikin sa ido 2,506 ne suka halarci kasar ta Togo, ciki hadda jami'ai 490 daga kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, da sauran wakilai daga kungiyar ECOWAS, da na kungiyar tarayyar tattalin arziki da kudade ta yammacin Afirka UEMOA a takaice, da ma wasu kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Kaza lika, bisa dokar zabe ta kasar Togo, ana gudanar da zagaye daya ne kadai, sa'an nan a bayyana wanda ya lashe zaben a matsayin sabon shugaban kasa, cikin kwanaki 6 da kammala kada kuri'un. (Maryam)