Rahotannin sun bayyana cewa an bude rumfunan zabe 8,994 a sassan kasar daban daban, inda ake sa ran 'yan kasar za su zabi ko dai shugaba mai ci Faure Gnassingbe, ko kuma daya daga sauran 'yan takara 4 da a wannan karo ke fatan a zabe su a mukamin shugabancin kasar.
Domin cimma nasarar zaben, wakilai 2,506 daga hukumomin kasa da kasa daban daban sun hallara a kasar ta Togo, inda za su sanya ido ga gudanar zaben. Cikin wannan adadi akwai wakilai kimanin 490 da suka fito daga kungiyar AU, da kungiyar ECOWAS da ta UEMOA da dai sauran su.
Shugaba Gnassingbe dai na neman sake kasancewar shugaban kasar ta Togo ne a karo na 3, bayan da ya lashe zaben kasar a shekarar 2005, da kuma zaben 2010. (Saminu)