Shugaba Joko Widodo yace shugabanni mahalarta taron daga yankin Asiya da Afrika sun yi aiki tukuru wajen samar da sahihanin matakai na karfafa zaman lafiya da lumana a duniya, da karfafa hadin gwiwwa dake tsakanin junan su, da dinke bambacin ci gabansu, da kuma tabbatar da ganin an tabbatar da samun 'yan cin kai ga Palestinu.
Haka kuma yace Mahalarta taron sun duba hanyoyin tabbatar da wadatar kudade don samar da anbaben more rayuwa a tsakanin kasashen yankin ta bankin zuba jarin raya ababen more rayuwa a yankin Asiya wato AIIB.
Mukaddashin shugaban taron kuma shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana taron a matsayin daya daga cikin taron tsakanin gwamnatoci kasashe wanda baya da nasaba da jadawalin MDD wanda kasashen Asiya da Afrika tare da sauran 'yan kallo suka halarta.
Taron kolin na yini biyu karkashin taken karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa domin samar da zaman lafiyar duniya da wadata, wani bangare ne na taron Asiya da Afrika na wannan shekara wanda ya hada kan shugabannin kasashen duniya da wakilai daga kasashen Asiya da Afrika guda 100, kasashe masu sa ido guda 15 sannan hukumomin kasa da kasa guda 17.( Fatimah)