A cikin makon guda, hukumomin za su yi amfani da zarafin su wajen gudanar da ayyuka kamar amsa tambayoyi, da gudanar da dandalin tattaunawa, da yin bayani a fili, da gabatar da rahoto, tare da bikin nune-nune da dai sauransu, don fadakar da ikon mallakar ilimi ga jama'ar kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, an samu bunkasuwa cikin sauri game da sha'anin ikon mallakar ilimi na kasar Sin a shekarun baya baya nan. Inda a shekarar 2014, yawan neman izinin mallakar fasaha a kasar Sin ya kai dubu 928, adadin da ya karu da kashi 12.5 cikin dari bisa na makamacin lokaci a shekarar 2013, kana ya ci gaba da kasancewa a matsayin farko a duniya a wannan fanni a shekaru hudu a jere.
Kaza lika yawan tambarin ciniki da aka yi rajista a wannan shekara ya kai miliyan 8 da dubu 390, adadin da ya kai matsayin farko a duniya a wannan fanni.
Shugaban hukumar kula da ikon mallakar ilimi ta kasar Sin Shen Changyu, ya bayyana cewa ikon mallakar ilimi muhimmin tushe ne, a fannin albarkatun neman samun bunkasuwa da yin takara, kana yana taka muhimmiyar rawa wajen daukar matakan kirkire-kirkire, da sa kaimi ga bunkasar tattalin arziki mai inganci. (Zainab)