in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta goyi bayan shigar da burin samun ilmi a duk rayuwar jama'a a cikin ajandar samun bunkasuwa bayan shekarar 2015
2014-09-25 15:42:47 cri
Mataimakin ministan kula da harkokin ilmi na kasar Sin Hao Ping ya bayyana a gun babban taro mai taken "mai da samun ilmi a gaban kome na duniya" a cibiyar MDD dake birnin New York a ranar 24 ga wata cewa, gwamnatin kasar Sin ta goyi bayan a mai da aikin tabbatar da dukkan jama'a sun samun ilmi mai inganci cikin adalci a duk rayuwarsu nan da shekarar 2030 a matsayin muhimmin buri a cikin ajandar samun bunkasuwa bayan shekarar 2015.

Hao Ping ya bayyana cewa, don cimma wannan buri, kamata ya yi a ba da muhimmanci wajen bunkasa harkar ilmi cikin dogon lokaci, da samar da ilmi cikin adalci, da inganta karfin malamai masu bada ilmi, da kuma mai da aikin bunkasuwar dalibai a dukkan fannoni a matsayin muhimmin tushe na ba da ilmi.

Ban da wannan kuma, Hao Ping ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin goyon baya ga kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka wajen raya aikin ba da ilmi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China