Madam Kawar ta ce, bisa bukatar Rasha, a wannan rana kwamitin sulhu ya yi shawarwari da ba a hukunce ba, inda Rasha ta rarraba wa membobin kwamitin sulhu wani daftarin kuduri dangane na na neman bukatar Saudiyya da sauran kasashe da su daina kai hare hare ta sama a kasar Yemen bisa la'akari da ra'ayin jin kai. Ta ce, membobin kwamitin sulhu na bukatar lokaci domin yin la'akari da wannan daftari, ana fatan za a fidda sakamako kafin ranar Litinin 6 ga wata.
A jiya, bisa jagorancin Saudiya, hadaddiyar rundunar sojan kasa da kasa ta kara kai jerin hare hare ta sama kan birnin Aden dake kudancin Yemen, domin taimakawa yakar dakarun kungiyar al-Ḥūthiyyūn.
Saudiya da sauran kasashe sun dakatar da zirga zirgar jirgin saman fasinja, tare da rufe tashoshin jirgin jiragen ruwa, dalilin hake ne ake fuskantar karancin kayayyakin bukatun yau da kullum a kasar. An samun dogon layin mutane a gaban tasoshin sayar da man fetur da dama, da kyar mutane ke samun sayen man fetur da man dizal domin biyan bukatunsu. Haka kuma yawan abincin da ake sayar a kasuwanni ya ragu.
A jiya kwamitin red cross na kasa da kasa ya bayyana cewa, hare hare ta sama da Saudiya da sauran kasashen kawancen suke kaiwai na babbar matsalakawo cikas wajen ga aikin jigilar kayayyakin agajin jin kai zuwa Yemen. Kafin wannan, kwamitin ya zargi kawancen kasashen da yunkurin hana jigilar kayayyakin agaji zuwa Yemen.(fatima)