in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in M.D.D. ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki kwararrun matakai don warware batun kwararowar 'yan gudun hijirar Yemen
2015-04-09 10:05:02 cri

Wani kwararre a fannin kare hakkin dan Adam dake aiki da ofishin M.D.D. mai suna Chaloka Beyani, ya yi kira ga kasashen duniya da su maida hankali ga batun kwararar 'yan gudun hijirar kasar Yemen.

Beyani, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a birnin New York, yana mai jaddada cewa, ko da yake ba a dakatar da kokarin da ake yi na shiga tsakani ba, a hannu guda yanayin da ake ciki a Yemen na kara tsananta, don haka kamata ya yi a kara azama sosai, kasancewar rashin hakan na iya kara yawan mutane dake rabuwa da gidajensu.

Bisa kididdigar da M.D.D. ta fitar, an ce rikicin siyasar kasar ta Yemen da aka kwashe makwanni biyu ana yi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 540, cikinsu har da yara 77, da fararen hula fiye da 300. Baya ga wasu kimanin 500 da suka jikkata. MDDr ta kuma bayyana cewa fiye da mutane dubu 100 ne suka kauracewa gidajensu.

Rahoto daga M.D.Dr. sun kuma bayyana cewa, an kai hare-hare kan asibitoci, da makarantu, da gidaje, tare da lalata manyan ayyukan samar da wutar lantarki, da ruwan sha da dama, kana dubun-dubantar mutane sun gujewa gidajensu. Kaza lika masu aikin ceto a kasar ta Yemen sun bayyana cewa, dakarun Houthi, da sojojin da ke goyon bayan shugaban Abd-Rabbu Mansour Hadi, na ci gaba da musayar wuta a birnin Aden dake yankin kudancin kasar.

Wani jami'in kiwon lafiya dake birnin Aden, ya gaya wa majiyar mu cewa, yanzu haka dakarun Houthi, da sojojin gwamnatin kasar na musayar wuta, a kokarin da bangarorin biyu ke yi na mallakar birnin Aden, lamarin da ya yi matukar lalata gine-ginen gwamnati. A daya hannun kuma akwai gidajen jama'a masu yawa da wuta ta kone sakamakon hare-haren igwa. Jami'in ya kuma ce a jiya Laraba, jiragen ruwan kungiyar ba da agaji ta Red Cross, sun isa tashar tekun Aden, sai dai sun kasa ba da agaji saboda kazantar rikicin. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China