Shugaba al-Sissi ya yi wadannan kalamai a lokacin da gamayyar kasashe goma da ke karkashin jagorantar Saudiyya ke kai hare hare ta sama kan mayakan shi'a na Houthis a kasar Yemen, wadanda suka karbe biranen kasar da dama tun cikin watan Satumban shekarar 2014 tare da tilastawa shugaban kasar Abd-Rabbu Manour Hadi ficewa daga kasar zuwa Riyad, hedkwatar kasar Saudiyya.
Rikicin Yemen na janyo fargaba sosai game da yiyuwar yankin mashigin ruwan Bab al-Mandab ya koma hannun mayakan Houthis da ake zaton samun goyon bayan kasar Iran da kuma ke janyo matsalar tsaro a kasashen da yankin Golfe. Kasar Iran dai ta yi watsi da zargin da ake mata na cewa tana baiwa mayakan shi'a makamai.
Kasashen Masar da Saudiyya sun tura jiragen ruwan yakinsu a mashigin ruwan Bab al-Mandab, wanda ita ce hanya guda wajen shiga yankin ruwan Suez tun daga ruwan tekun Arabic da ya kasance muhimmin wurin musanyar kasuwanci tsakanin Turai da Asiya. (Maman Ada)