150326-shugaban-hukumar-bincike-ta-kwamitin-ioc-ya-iso-birnin-beijing-zainab.m4a
|
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin, kuma shugaban hukumar wasanni ta kasar Sin Liu Peng, da shugaban kwamitin neman iznin daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing a shekarar 2022, kuma magajin birnin Beijing Wang Anshun ne suka taryi Mr. Alexander a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake nan Beijing.
Ya zuwa yanzu, dukkan mambobin tawagar bincike ta kwamitin IOC sun iso birnin Beijing, kuma sun fara gudanar da bincike kan birnin Beijing, da ma Zhangjiakou tun daga ranar Talata 24 ga wata.
Tawagar bincike da ta zo birnin Beijing ta kunshi mutane 19, ciki har da membobin kwamitin IOC guda hudu, wato Alexander Zhukov daga kasar Rasha, da Barry Maister daga New Zealand, da Adam Pengilly daga Britaniya, da kuma Tsunekazu Takeda daga kasar Japan.
Yayin da membobin tawagar binciken suke gudanar da aikin su a nan Beijing da Zhangjiakou, za su saurari bayanai da kwamitin wasannin Olympics na Beijing zai gabatar musu, za kuma su ziyarci wuraren da za a gudanar da wasanni, su amsa tambayoyin da za a yi musu, tare da tattaunawa da juna da dai sauransu. Ta haka ne kuma za su gano halin da ake ciki, game da batun neman iznin daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 da Beijing da Zhangjiakou ke nema.
Kaza lika tawagar za ta yi bincike kan filayen wasanni, da dakunan wasannin da za a yi amfani da su a yayin wasannin a Beijing wadanda suke Yanqing da kuma Zhangjiakou. Bayan kammala binciken, tawagar za ta duba rahoton neman iznin daukar bakuncin wasannin Olympics na Beijing, da kuma abubuwan da suka gano, su kuma rubuta rahoton bincike, su gabatar da shi ga kwamitin IOC, daga baya kuma za a bayar da ra'ayin IOC ga biranen da suke neman iznin daukar bakuncin wasannin.(Zainab)