in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya ya nuna gamsuwa ga shirin gudanar gasar Olympics ta birnin Rio
2015-03-12 14:44:41 cri
Bayan kammala duba yanayin da ake ciki a kasar Brazil cikin wa'adin mako guda, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya Thomas Bach, ya bayyanawa 'yan jarida gamsuwar sa, game da ayyukan da ake gudanarwa, game da shirya gasar Olympics ta birnin Rio de Janeiro, wadda ke tafe a shekarar 2016, ko da yake ya ce ana bukatar kara azama game da hakan.

A daya hannun kuwa, wasu masu zanga-zanga sun yi gangami a kofar otel din da aka gudanar da taron manema labarum, inda suka nuna rashin jin dadin su, game da yadda gine-gine dakunan wasannin da aka yi suka lalata muhallin halittu dake kewayen wuraren.

Game da wannan batu, Bach ya bayyanawa 'yan jarida cewa, kwamitin wasannin Olympics na duniya IOC yana fatan sauraro, da tattaunawa da jama'a, da burin amsa tambayoyin su yadda ya kamata.

Ban da wannan kuma, Bach ya sanar da cewa, za a kebe wani yanki na nuna alhini ga iyalai da abokan 'yan wasan da suka rasu, a wani yanki da 'yan wasa masu halartar gasar Olympics din zasu zauna, yankin da zai zamo irin sa na farko a tarihi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China