in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya nuna damuwa game da hasarar rayukan mutane sakamakon matakan soji da aka dauka a kasar Yemen
2015-04-01 10:25:32 cri
A ranar Talatannan, sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-Moon yaba da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya bayyana damuwarsa game da hasarar rayukan mutane sakamakon matakan soji da aka dauka a kasar Yemen. Sanarwar ta ce, Ban Ki-Moon ya ja kunnen bangarorin daban-daban da suke daukan matakan soji a Yemen da su bi dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, don tabbatar da tsaron jama'a. Ya kuma jaddada a kiyaye asibiti da sauran na'urorin ba da aikin jinya bisa dokokin kasa da kasa, gami da sake nanata muhimmancin warware rikicin kasar cikin lumana.

A wannan rana kuma, kakakin sojin kasar Saudiyya ya ce, yanzu kasar da sauran kawancen kasashe ba su da shirin tura sojojin kasa zuwa kasar Yemen, amma a shirye suke ne don shiga cikin yaki.

Ranar Talata rana ce da aka fi yi arangama da juna a tsakanin sojojin Saudiyya da dakarun masu dauke da makamai na Houthi.A lokacin wannan arangama bangarorin biyu sun yi amfani da motocin igwa da rokoki wajen kai farmaki ga juna a kan iyakar kasashen Saudiyya da Yemen. A wannan rana kuma, yayin da ministan harkokin wajen Yemen Aden Yasin ke zantawa da gidan talibijin Saudiyya, ya yi kira ga kawacen sojoji da su gaggauta tura sojojin kasa a kasarsa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China