in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron koli kan hanyar Siliki ta ruwa ta karni na 21
2015-02-12 16:44:37 cri

An gudanar da taron koli na tattaunawa kan hanyar Siliki ta ruwa ta karni na 21 a ranar 12 ga wata a birnin Quanzhou dake lardin Fujian na kasar Sin, dake mafarin hanyar. Mamban hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma babban jami'i mai kula da watsa labarai Liu Qibao ya halarci taron tare da yin wani jawabi.

A cikin jawabinsa, Liu Qibao ya gabatar da shawarwari biyar, wato kafa hanyar fahimtar juna ta bude kofa a tsakanin kasashen dake kan hanyar, da hanyar samun moriyar juna da hadin gwiwa, da hanyar shimfida zaman lafiya da jituwa, da hanyar sada zumunta da koyi da juna, da kuma hanyar cimma buri tare. Ta haka, za a sake inganta hanyar Siliki ta ruwa wadda ta ratsa nahiyoyin Asiya, Afirka da Turai. Hanyar da aka yi amfani da ita wajen samun alfanu mai yawa, da kuma sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashe daban daban a shekaru 2000 da suka wuce. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China