Da yammacin jiya Alhamis ne shugabannin kafofin watsa labarun kasashe daban daban, sun amince da kuma sa hannu kan wata takardar "bunkasa Hanyar Siliki" a lardin Hainan na kasar Sin, inda suka yi alkawarin tabbatar da tsarin yin musayar ra'ayi akai-akai, domin kara cudanyar ma'aikata, da more albarkatunsu, da kuma neman sabuwar hanyar hadin gwiwarsu. Sannan nan za su nemi wani lokacin da ya dace wajen kafa kungiyar hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban da shirin zirin tattalin arziki na siliki, da hanyar siliki ta ruwa ta karni na 21 ya shafa.
A gun bikin sanya hannu kan takardar, shugaban kwamitin harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana cewa, jama'ar kasashe daban daban da "shirin ziri daya hanya daya" ya shafa ke da moriyar bai-daya, don haka shirin zai amfana wa dukkansu. A ciki, kafofin watsa labaru na kasashe daban daban za su samu kyakkyawar damar bayar da amfaninsu.
Haka zakila, a matsayin wakilin bangaren dake jagorantar aikin kulla takardar ta " Bunkasa Hanyar Siliki", shugaban gidan rediyon kasar Sin wato CRI Wang Gengnian, ya karanta sakon dake kunshe cikin takardar. Inda ya bayyana cewa, domin tinkarar sabbin kalubaloli, dole ne kafofin watsa labaru su yi watsi da tsohon ra'ayinsu, sannan nan su hada gwiwa cikin yakini, domin neman samun bunkasuwa mai dorewa, ta yadda za a iya kafa wani sabon tsarin hadin kansu da na yin hakuri da juna, a kokarin samun nasara tare.(Lami)