Tsarin aiwatar da wannan manufa dai na kunshe ne da manufofin bunkasa tattalin arzikin yankin Siliki, da kuma na bunkasa hanyar siliki ta ruwa a karni na 21, tsari ne da kuma shugaba Xi ya gabatar tun cikin shekara ta 2013.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar aiwatar da gyare-gyare, da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, da kuma ma'aikatar cinikayya ne suka fitar da cikakken tsarin aiwatar da wadannan manufofi biyu.
Ana sa ran wannan mataki zai bada damar inganta gudanar harkokin tattalin arziki, da daidaito a fannin samar da albarkatu, tare da hade kasuwanni ta hanyar hade yankunan nahiyar Asiya, da Turai da kuma Afirka.
Kaza lika tsarin zai baiwa daukacin kasashen duniya, da ma hukumomin kasa da kasa damar shiga a dama da su, cikin harkokin tattalin arziki bisa mutunta juna da kokarin samun moriya ta bai daya.
Bugu da kari tsarin ya yi kira da a tuntubi juna wajen tsara manufofi da hada na'urorin juna, baya ga kauda shingen cinikayya, da hade sassan kasuwanci waje guda da kuma kulla dangantakar al'ummomi daban daban, karkashin tsarin domin cimma moriyar albarkatun juna, bisa tsarin hadin gwiwar kasashe da jigo daban daban.(Saminu Alhassan)