in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 na kunshe da fatan kasashen gabas ta tsakiya
2015-04-08 10:55:22 cri
Manzon musamman na kasar Sin mai kula da harkokin gabas ta tsakiya jakada Gong Xiaosheng, wanda ke ziyarar aiki a kasar Iran, ya bayyana cewa, shirin zirin tattalin arziki na siliki, da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, na kunshe da burin kasashen gabas ta tsakiya, kuma yana da goyon bayan gamayyar kasashen duniya.

Mr. Gong wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron maneman labarai, ya ce kafin kasar Sin ta fidda wannan shiri, wasu kasashen gabas ta tsakiya da dama sun gabatar da shirin farfado da hanyar siliki, kana, kasashen sun yi musayar ra'ayi dangane da hakan. A daya bangaren kuma fidda shirin da Sin ta yi, ya karawa kasashen fahimtar fannoni da za a iya hadin gwiwa ta cikin su.

Bugu da kari, lokacin da yake tsokaci game da kalubalolin da rikicin yankin gabas ta tsakiya zai iya haifarwa ga gudanarwar wannan shiri, Gong Xiaosheng ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya sha fama da tashe-tashen hankula, amma bai kamata a zurawa rikicin yankin ido ba kawai, duba da cewa duk da wannan kalubale, yankin na da damar samun bunkasuwa.

Dangane da babban sakamakon da aka samu game da batun nukiliyar kasar Iran a 'yan kwanankin nan, Gong Xiaosheng ya ce, warware matsalar nukiliyar kasar Iran na da muhimmiyar ma'ana ga kasar Iran, baya ga kasancewarsa ta sa kaimi ga warware sauran matsalolin da yankin ke fuskanta ta hanyoyin shawarwari da siyasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China