Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, babban sakataren kwalejin ilmin zamantakewar al'umma na kasar Sin, kuma babban editan mujallar ilimin zamantakewar al'ummar kasar Sin Gao Xiang, ya tabo batun dangantakar dake tsakanin hanyar siliki ta ruwa, da mu'amalar al'adu daga fannoni uku.
Ciki akwai batun mu'amalar al'adu a tsakanin kasa da kasa, wanda ya bayyana a matsayin dadadden sha'ani game da tarihin hanyar siliki ta ruwa, wanda kuma zai taimakawa wajen raya hanyar siliki. Ya ce raya hanyar siliki ta ruwa yana bukatar ilimin al'adu, da zamantakewar al'umma.
A karshe Mr. Gao Xiang ya bayyana cewa, ya kamata a kara kiyaye al'adu daban daban, da kara kyautata mu'amala a tsakanin al'adu daban daban, da amfani da fifikon da mu'amalar al'adu ke da shi wajen raya hanyar siliki ta ruwa ta karni na 21 yadda ya kamata. (Zainab)