Kaza lika sanarwar ta yi Allah-wadai da lalata yunkurin siyasar kasar ta Yemen da dakarun Houthi ke yi, matakin da kwamitin tsaron ya ce ya haifar da babbar illa ga sha'anin tsaro, da zaman lumana, da mulkin kai, da aikin dinke-barakar kasar. Har wa yau kwamitin ya bukaci dakarun Houthi da su janye jiki daga hukumomin kasar.
A daya hannun kuma, kwamitin sulhun M.D.D. ya sake nanata kudurin daukar matakin da ya dace, kan duk bangaren da ya ki martaba wannan umarni.
Bugu da kari kwamitin sulhun ya yi kakkausar suka game da harin sama, da aka kai ga fadar shugaban kasar, da babban filin jiragen saman kasar da ke birnin Aden, hedkwatar kasar, da ma sauran hare-haren da aka kaddamar a ranar Juma'ar da ta gabata, ya kuma bukaci bangarorin da abin ya shafa da su kauracewa amfani da makamai, da tada hargitsi a kasar.
Kwamitin sulhun ya nemi dakarun Houthi, da sauran bangarorin da rikicin kasar ya shafa da su gaggauta shiga shawarwarin MDD, na kawar da sabanin da ke tsakaninsu, su kuma yi adawa da duk wani mataki na rura wutar rikici domin cimma muradun siyasa a kasar. (Bako)