Mr. Zhang ya fadi haka ne a yayin taron tattauna kan yadda za a raya "zirin tattalin arziki dake kan hanyar siliki" da "sabuwar hanyar siliki dake kan teku na karni na 21" da aka shirya a birnin Xi'an dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Mr. Zhang Gaoli ya bayyana cewa, a lokacin da ake aiwatar da manufar raya "ziri daya da hanya daya", dole ne a yi kokarin yin mu'amala da juna, da kuma karfafa hadin gwiwa da kasashe wadanda suke cikin zirin da kuma hanyar. Sannan dole ne a yi kokarin samar da muhimman ayyukan more rayuwa, kara bunkasa masana'antu masu inganci, da kuma kara yin hadin gwiwa a fannonin masana'antun samar da albarkatun hallitu, aikin gona na zamani, sana'ar kere-kere ta zamani, da hidimomin zamani da kuma tattalin arzikin teku. Bugu da kari, ya kamata a kara yin hadin gwiwa irin ta moriyar juna domin ta yadda za su kasance tare tamkar wata kungiyar da juna za su mora, da sauke nauyi tare da cimma buri iri daya. (Sanusi Chen)