in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gana da Ministan harkokin wajen Rasha
2015-02-02 20:32:56 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Sergei Lavrov a ranar litinin din nan a Birnin Beijing inda bangarorin biyu suka jadadda kudurinsu na kara hadin kai da juna a kan harkokin duniya baki daya.

Shugaba Xi ya ce kasashen biyu ya kamata su hada hannu waje daya da sauran kasashen duniya domin bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu da za'a yi a wannan shekarar.

Yace kasar Sin zata hada kai da Rasha wajen taron BRICS da za'a yi a Rashan bana domin cigaba da bada goyon baya ga farfadowar tattalin arziki na kasashe mambobi da ma duniya baki daya.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen Lavrov ya isar da sakon fatan alheri daga wajen Shugaba Putin, yana mai cewa hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu yana da muhimmancin gaske ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya baki daya.

Sergei Lavrov dai ya zo nan birnin Beijing ne saboda taro na tuntubar juna tsakanin ministocin harkokin wajen kashen Rashan, Sin da Indiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China