in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Amurka ya yi kira da a yi kokarin kawar da barazanar da kungiyar IS ke kawowa
2015-04-07 10:53:17 cri

Mataimakin sakataren harkokin waje ta kasar Amurka Anthony Blinken, ya yi kira ga kasashen duniya da su yi kokari tare, wajen yaki da 'yan ta'adda domin kawar da barazanar da kungiyar IS da sauran kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ke kawowa.

Blinken ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a birnin Beirut na kasar Lebanon, yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar.

Mr. Blinken ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri, da firaministan kasar Tammam Salam, da kuma ministan harkokin wajen kasar Gebran Bassil.

Yayin zantawarsa da manema labaru bayan ganawarsa da kusoshin gwamnatin kasar, Mr. Blinken ya ce baya ga bukatar daukar matakin soja wajen yaki da 'yan ta'adda, a daya hannun kamata ya yi kasashe daban daban, su hana al'ummunsu ba da tallafi, da kuma shiga wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda.

Ya kara da cewa, rikicin kasar Sham ya haifar da mummunan tasiri ga kasar Lebanon, don haka ne ma kasar Amurka ke jinjinawa kokarin da gwamnatin Lebanon, da kuma al'ummar kasar ke yi wajen karbar 'yan gudun hijirar kasar Sham.

Ya ce Amurka za ta ci gaba da taimakawa hukumomin tsaron kasar ta Lebanon, wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China