in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bukatar kasashen duniya su yi tarayya wajen kawar da ta'addanci, a cewar ministan al'adun kasar Iran
2015-03-25 16:02:55 cri
Ministan ma'aikatar al'adu da lura da shiriyar musulunci na kasar Iran Ali Janati, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada da juna wajen yaki da ta'addanci, yana mai cewa akwai bukatar gwamnatocin kasa da kasa su yi kokari tare don kawar da ta'addanci.

Janati ya bayyana hakan ne a birnin Beirut, yayin wata ziyarar aiki da ya gudanar a kasar Lebanon a jiya Talata. Yayin ziyarar ministan ya gana da firaministan kasar Lebanon Tammam Salam, da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri, kafin ya gana da 'yan jarida.

A zantawarsa da manema labarun, ya bayyana musu cewa ya tattauna ne da shuganannin kasar Lebanon, game da barazanar da ta'addanci ke haifarwa kasashen Iraki, da Syria, da Lebanon, har ma a dukkan yankin baki daya.

Janati ya kara da cewa ta'addanci ya haifar da babbar illa ga zaman lafiya a kasar Lebanon, da sauran kasashen dake yankin, da ma dukkan duniya baki daya. Ya ce kamata ya yi gwamnatocin kasashen duniya da jama'arsu su yi kokari tare don kawar da ta'addanci.

Haka zalika, Janati ya bayyana cewa, kasar Iran na goyon bayan Lebanon a fannin daukar matakan tabbatar da zaman lafiya da zaman karko, da kuma dawo da hadin kan kabilun kasar. Ya ce, kasar Iran na daukar zaman lafiyar kasar Lebanon tamkar nata, duba da cewa halin da ake ciki a kasar Lebanon na yin babban tasiri ga zaman lafiyar dukkan yankin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China