in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kira taron kolin kasa da kasa game da yaki da ta'addanci
2015-02-20 16:27:59 cri
A jiya Alhamis ne aka shiga rana ta uku, ta taron kolin duniya da kasar Amurka ta kira game da yaki da ta'addanci.

Yayin zaman na jiya, wakilai daga Faransa, da Jordan, da Masar, da Japan da na sauran kasashe sun gabatar da jawabansu, inda suka jaddada aniyar su ta ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci. Hakan kuwa na zuwa ne 'yan kwanaki kadan, bayan da dakarun kungiyar IS suka hallaka 'yan asalin wadannan kasashe dake halartar taron.

A jawabinsa babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada gwiwa wajen yaki da ayyukan ta'addanci, bisa kuduri na 2178, wanda kwamitin sulhun MDDr ya zartas a watan Satumbar bara.

Shi kuwa a nasa bangare shugaba Barack Obama na Amurka, ya sake jaddada cewa, kasashen yammacin duniya ba sa nuna kiyayya ga addinin musulunci, kana ya yi kira ga al'ummar duniya da ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin kawar da wannan zargi dake bazuwa.

A daya hannun kuma, sanarwar bayan taron ta bayyana amincewar kasashe mahalarta taron na wannan karo, game da sake haduwa a babban taron MDD dake tafe cikin watan Satumba mai zuwa a birnin New York, domin ci gaba da shawarwari kan yadda za a kawo karshen matsalar ta'addanci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China