A jiya Laraba ne dai Liu Jieyi ya kira wani taron kwamitin sulhun MDD, inda aka nazarci yanayin da ake ciki a kasar Libya. Kaza lika kwamitin sulhun ya saurari rahoton da wakilin musamman na babban sakataren MDD kan batun Libya Bernardino Leon ya gabatar ta kafar bidiyo.
Taron dai ya samu halartar ministocin harkokin wajen Libya, da Masar, da wakilin kasar Algeria, inda suka gabatar da jawabai. Har wa yau mambobin kwamitin sulhun sun yi wata ganawar sirri game da halin da kasar Libiya ke ciki.
Jim kada da kammala taron, Liu ya bayyana cewa, membobin kwamitin sulhun sun yi Allah wadai da danyen aikin da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta yi, na kashe wasu Misirawa wadanda ta yi garkuwa da su, tare da mika sakon ta'aziya ga gwamnatin Masar da iyalan wadanda aka hallaka.(Fatima)