A yayin taro karo na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 12 da ke gudana a nan birnin Beijing, mista Wang Yi ya amsa tambayar 'yan jarida a yayin da ya kira wani taron menama labaru, cewa, a ganinmu, abin dake gaban kome na yaki da ta'addanci shi ne kawar da yanayin dake haifar da ta'addanci. Ba za mu iya kawar da ta'addanci ba, muddin sai mun sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki, da daidaita rikicin shiyya-shiyya, da yin shawarwari cikin adalci tsakanin al'adu da addinai da al'ummomi iri daban daban.
Bayan haka, Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ita ma ta sha wahalhalu sakamakon ta'addanci, yanzu tana fuskantar barazanar kungiyar "East Turkestan Islamic Movement" (ETIM). Za mu tinkari sabuwar barazana da sabon kalubale da ta'addanci zai kawo tare da sauran kasashen duniya bisa tsarin girmama juna da hadin gwiwa cikin adalci.(Fatima)