Game da halin da ake ciki, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, an shiga matakin karshe don gane da shawarwarin, kuma kasar Sin na fatan bangarori da abin ya shafa za su iya gaggauta kaiwa ga cimma cikakkiyar yarjejeniya kan batun.
Bisa labaran dake fitowa daga zaman, ya zuwa yanzu ba a kai ga cimma yarjejeniyar da ake fata bisa lokacin da aka tsara ba, watau ya zuwa wa'adin ranar 31 ga watan Maris, don haka ne ma kasashen shida da batun nukiliyar kasar ta Iran ya shafa da ita kanta kasar Iran din suke ci gaba da gudanar da shawarwari har ya zuwa jiya Laraba.
An dai sake bude taron shawarwarin ne na wannan karo a ranar 26 ga watan Maris, bayan aka dakatar da hakan a ranar 20 ga watan Maris a birnin na Lausanne. Haka kuma, an ce shawarwarin sun kasance masu matukar muhimmanci dake wakana a lokaci na musamman. (Maryam)