in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya isa kasar Suise domin halarta taro kan nukiliyan kasar Iran
2015-03-29 15:18:24 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tashi a ranar Asabar zuwa kasar Suise domin halartar wani taron ministoci kan batun nukuliyar kasar Iran.

Za'a bude wannan taro dai a ranar yau Lahadi a birnin Lausanne na kasar Suise, a cewar wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin waje.

Wani sabon zagayen shawrawari ya fara a ranar Alhamis tsakaninn Iran da gungun kasashe masu fada a ji kan wannan batu da suka hada da Amurka, Sin, Rasha, Faransa, Ingila da Jamus, domin kokarin cimma wata yarjejeniyar ke nan da karshen wata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China