Kwamitin sulhu na MDD ya nuna juyayi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, da kuma jama'a da gwamnatin kasar Kenya, haka kuma, kwamitin sulhu na MDD ya yaba wa gwamnatin kasar Kenya kan kokarin da take bayar wajen yaki da ta'adanci da kuma gudummawa da ta bayar kan aikin yaki da kungiyar Al-Shabaab na tawagar musamman da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU ta tura zuwa kasar Somaliya.
Bugu da kari, kwamitin sulhu na MDD ya sake jaddada cewa, zai mai da martani kan kudurin aikace-aikacen ta'addanci, bisa kundin tsarin MDD.
A ranar 2 ga wata, wasu dakaru sun kai hari a jami'ar Moi dake birnin Garissa dake arewa maso gabashin kasar Kenya, inda suka halaka mutane 148, yayin da 179 suka ji rauni, sa'an nan, kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da daukar alhakin harin din, kana harin ya kasance harin ta'adanci mafi tsanani da kasar Kenya ta taba fama da shi, tun shekarar 2011 da kasar ta tura sojoji zuwa kasar Somaliya domin yaki da dakarun kungiyar Al-Shabaab. (Maryam)