in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin musulmi a Kenya sun yi allawadai da harin ta'addanci a Garissa
2015-04-04 15:58:37 cri
Shugabannin addinin Musulunci a kasar Kenya sun yi allawadai a ranar Jumma'a da harin ta'addancin da kungiyar Al Shebab ta kasar Somaliya ta kai a jami'ar Garissa dake arewa maso gabashin kasar Kenya, wanda ya halaka dalibai 148 tare da raunana wasu da dama. Da suke bayani gaban manema labarai a birnin Garissa, shugannin musulman sun jaddada raba gari da masu kaifin kishin Islama dake tuzarta addinin musulunci ta hanyar aikata miyagun laifuffukan kisa. Al'ummar musulmi baki daya dake birnin Garissa suna allawadai da babbar murya da wadannan ayyuka na fitar da hankali da aka aikata kan daliban da ba su ji ba su gani ba. Muna aika ta'aziyarmu ga iyalan mamatan, in ji malam Abdullah Salat, shugaban kwamitin koli na musulman kasar Kenya reshen Garissa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China