in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta kashe mutanen Iraki 43
2015-02-22 16:10:22 cri
Rahotanni daga hukumar tsaro ta Iraki, na cewa, a ranar Aasabar din nan, 'yan kungiyar IS sun kashe 'yan Iraki 43 a jihar al-Anbar dake yammacin kasar.

Wani mai bayar da sako ga hukumar tsaro ta jihar al-Anbar ya bayyana cewa, 'yan kungiyar IS sun cafke mutanen ne '

yan darikar Sunni yayin da suka yi musayar wuta da sojojin Iraki a garin Baghdadi dake yammacin jihar al-Anbar sannan suka mika wadanda suka cafken su zuwa birnin Heet dake hannun kungiyar IS, inda aka sa su cikin kejin karfe tare da cinna masu musu wuta.

Wannan mutum ya kara da cewa, a wannan rana kuma, 'yan kungiyar IS sun kewaye wani wata unguwar da daruruwan iyalai na sojojin Iraki da na dakarufararen hula sama da dari daya ke zama a garin Baghdadi, wadanda kuma suke fama da matsalar karancin makamai da abinci da kuma ruwan sha.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China