Kakakin majalisar jama'ar kasar Omar Hemeidan ya bayyana wa 'yan jarida cewa, 'yan majalisar 74 a cikin dukkan 'yan majalisar 85 sun amince da sauke Al-Hasi daga mukaminsa. Kana majalisar ta tsaida kuduri a wannan rana cewa, mataimakin firaministan gwamnatin ya gudanar da ayyukan firaministan kafin aka zabi sabo.
Amma Hemeidan bai yi bayani game da dalilin da ya sa aka sauke Al-Hasi daga mukaminsa ba. A kwanakin baya dai an zargi ministocin gwamnatin Al-Hasi da dama da cin hanci da rashawa, amma Al-Hasi bai sauke su daga mukamansu ba, don haka aka nuna rashin jin dadi game da hakan. (Zainab)