Wakilin musamman na babban satakaren MDD mai kula da batun Libya Bernardino Leon ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, wannan taro yana da muhimmanci sosai, don haka tilas ne shugabannin bangarori daban daban na kasar Libya su yi kokarin shimfida zaman lafiya. Ana sa ran masu halartar taron za su bullo da matakan da za su kai ga warware rikicin kasar, da kafa tsarin demokuradiyya da kawar da ayyukan ta'addanci.
Ban da wannan kuma, Leon ya bayyana cewa, taron wata alama ce da ke nuna cewa, bangarori daban daban da rikicin kasar Libya ya shafa, sun fahimci cewa, yin shawarwari cikin lumana ita ce hanya mafi dacewa wajen warware rikicin kasar, ganin yadda ayyukan ta'addanci ke kara haddasa barazana ga samun dinkuwar kasar. Kana ya ce, MDD ta nuna goyon baya ga bangarorin kasar daban daban da su yi shawarwari ba tare da gindaya wani sharadi ba. (Zainab)