in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren sojan kasar Libya da dakaru masu tsattsauran ra'ayi sun yi musayar wuta a gabashin kasar
2015-02-04 10:58:43 cri
Wani jami'in bangaren soja na kasar Libya ya bayyana a ranar 3 ga wata cewa, tun a ranar 2 ga wata ne sojojin kasar suke yin musayar wuta da dakaru masu tsattsauran ra'ayin kishin addini a dab da birnin Derna na gabashin kasar , lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 11.

Kakakin sojojin kasar Libya Ahmad Al-Mismari ya bayyana cewa, tun a ranar Litinin ne sojojin kasar suka rika kai hare-hare kan sansanin dakaru masu tsattsauran ra'ayin kishin addini dake dab da birnin a yunkurin kwace birnin Derna. Ya zuwa yanzu, sojoji 11 sun mutu a sakamakon gwabzawar, kana wasu sojoji 25 sun ji rauni. Al-Mismari ya ce, dakaru masu tsattsauran ra'ayi da dama sun mutu ko raunata a sakamakon hare-haren, amma ba a san adadinsu ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China