in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Libya sun kai hari ta sama kan jirgin ruwa na kasar Greece
2015-01-06 11:54:24 cri
Rundunar sojojin dake karkashin gwamnatin wucin gadi ta kasar Libya ta amince da cewa, mayakanta na sama sun kai farmaki ta sama kan wani jirgin ruwan jigilar man fetur na kasar Greece a birnin Derna dake bakin teku a gabashin kasar Libya.

Kakakin rundunar sojan kasar Ahmad Al-Mismari ya bayyana haka ne a ranar 5 ga wata, inda ya ce wannan jirgin ruwa dake dauke da tutar kasar Liberia ya daure mana kai, saboda haka sojojin Libya sun umurce shi da ya tsaya kafin ya shiga tashar ruwan Derna, domin a gudanar da bincike ko akwai makamai a cikinsa. Bayan jirgin ya ki bin umurnin ne, mayakan saman suka afka masa hari.

A nata bangare, ma'aikatar harkokin wajen kasar Greece ta bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ta kai suka sosai kan wannan lamarin. Sanarwar ta ce, akwai ma'aikata 26 a cikin jirgin a lokacin, lamarin da ya haddasa mutuwar ma'aikata biyu, yayin da wasu biyu suka ji rauni. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China