in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasashen waje 5 sun mutu sakamakon harin da aka kai wani otel a Libya
2015-01-28 15:06:24 cri
Wani harin Bam da aka kaddamar kan wani Otel dake birnin Tripoli na kasar Libya, ya hallaka mutane 9, ciki har da 'yan kasashen ketare 5 da ma'aikatan Otel din 3.

Rahotanni sun bayyana cewa cikin wadanda harin ya rutsa da su, akwai Ba'amurke daya, da dan Faransa daya, da mutum guda daga Koriya ta kudu, da kuma mutane biyu daga Philippines.

Tuni dai reshen kungiyar IS dake kasar ta Libya ya bayyana daukar nauyin kai wannan hari.

Da misalin karfe 10 na safiyar Talata ne dai wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse daf da Otal din Corinthia, sa'an nan wasu dakaru dauke da bindigogi su 3, suka kutsa kai cikin otel din, suka kuma harbe bakin 'yan kasar waje su 5.

Jim kadan da aukuwar lamarin, sojojin gwamnatin kasar sun kewaye otel din, tare da debe sauran mutanen dake cikin otel zuwa wani wuri na daban don basu kariya. An kuma ce sojojin sun yi musayar wuta tare da maharan. A karshe dakarun sun tada wasu bama-bamai da suka dana a jikin su, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar su, tare da wani mutum guda da suka yi garkuwa da shi.

Game da aukuwar wannan lamari, kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwa a ranar Talata, ya na mai Allah wadai da wannan hari na birnin Tripoli. Sanarwar ta kuma jaddada wajibcin ci gaba da yaki da duk wani nau'in ayyukan ta'addanci.

Har wa yau kwamitin sulhu ya ce, ya zama wajibi a cafke tare da gurfanar da wadanda suka shirya, da masu goyon baya wannan aikin ta'addanci gaban kuliya. Sanarwar ta kuma bukaci daukacin kasashen duniya dasu hada gwiwa da hukumomin Libya wajen warware rikicin kasar bisa dokokin kasa da kasa, karkashin kudurin kwamitin sulhu mai alaka da batun. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China