in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na MDD ya fara aikin shiga-tsakani domin farfado da shawarwari kan batun Libya
2015-01-10 17:08:57 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libya, ta fitar da wata sanarwa a jiya Jumma'a, dake cewa wakilin musamman na babban magatakardan MDD kan batun kasar Libya, Mista Bernardo Leon, ya ziyarci biranen kasar Libiya da dama, a wani mataki na janyo hankulan masu ruwa da tsaki, game da gaggauta farfado da shawarwari.

Yayin da yake ganawa da bangarorin kasar daban-daban, Mista Bernardo ya jaddada cewa kamata yayi, a gaggauta komawa teburin shawarwari ba tare da wani bata lokaci ba.

Kaza lika ya yi gargadi cewa ci gaba da dage shawarwarin, ka iya haifar da karin matsaloli wajen cimma matsaya guda kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da batun kawo karshen musayar wuta, da sake gina tsarin siyasar kasar. Har wa yau, Mista Bernardo ya bukaci bangarorin da su dakatar da bude wuta, don samar da yanayi da zai bada damar gudanar da shawarwari.

Bisa kokarin shiga-tsakanin da MDD tayi, bangarorin dake adawa da juna a Libya sun tattauna a zagaye na farko, a ranar 29 ga watan Satumbar bara a garin Ghadamis, inda suka cimma maslaha kan tsagaita bude wuta nan take, sai dai ya zuwa yanzu kura bata lafa ba, kana an yi ta dage gudanar sabbin shawarwari, saboda ko-in-kula, da bangarorin da abin ya shafa ke nunawa. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China