in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Zambia sun jaddada ci gaba dangantakar kasashensu
2015-03-30 20:40:59 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Zambia Edgar Lungu a babban dakin jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing, ganawar da ta gudana a yau Litinin 30 ga wata.

A zantawar shugabannin biyu sun jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu, su kara martaba zumuncin gargajiya dake tsakanin su, yayin da suke zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, domin tallafawa jama'ar kasashen biyu.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da hadin gwiwa, da kuma taimakawa kasashen Afirka, wajen shimfida zaman lafiya na dindindin, da kuma samun dauwamammen ci gaba. Kuma a bana ake cika shekaru 15 da kafuwar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika, kana za a gudanar da taron ministoci karo na shida a kasar Afirka ta Kudu, inda kasar Sin ke fatan gudanar da hadin gwiwa da kasar Zambia, da sauran mambobin taron, domin karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka, da kuma ciyar da harkokin cimma moriyar juna gaba.

A nasa bangare kuwa, Mr.Lungu ya bayyana fatan karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka bisa tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, ya ce kasashen Afirka na maraba da manufofin tattalin arziki na kasar Sin, ganin yadda take bude kofa ga kasashen waje, da dukufa kan dunkulewar yankin. Daga nan sai ya yi fatan kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka wajen samun ci gaba.

A daya hannu shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaba Lungu a dai wannan rana ta Litinin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China