A yayin taron manema labaran da aka shirya, mukaddashin babban alkalin kasar ya bayyana cewa, yawan mutanen da suka kada kuri'u a yayin zaben shugaban kasa a wanann karon ya kai kashi 32.36 bisa 100, adadin da ya kasa da na zaben shugaban kasa na karon da ya gabata, dake kashi 50 bisa 100.
Haka kuma a yayin wani taron manema labarai, dan takarar kawancen adawa na UPND, Hakainde Hichilema ya bayyana cewa, sakamakon zaben gaskiya bai nuna fatan al'ummar kasar ba, tare zargin jam'iyyar mai mulki da tafka magudi a yayin zaben.
Dangane da lamarin, shugaban kwamitin kula da harkokin zaben kasa ya bayyana cewa, an taba canja lokacin yin kididdigar kuri'u da aka kada sabo da dalilin dake shafar yanayi, amma babu shakka an gudanar da babban zaben shugaban kasa na wannan karo ba tare da boye kome ba da kuma cikin yanayin adalci. (Maryam)