A cikin sakon, shugaba Xi ya bayyana cewa, a tsawon rayuwarsa, shugaba Sata ya dora muhimmanci kan bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin Sin da Zambia. A lokacin da ya ke shugabancin kasar, an kara sada zumunci da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.
Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin ta dora muhimmanci kan raya dangantaka tsakanin kasashen biyu. Kuma ya yi imani cewa, bisa kokarin gwamnatoci da jama'ar kasashen biyu ke yi, za a kara samun kyaututuwar kyakkyawar dangantaka da dankon zumunci a tsakaninsu.(Fatima)