Edgar Lungu, wanda shi ne dan takarar jam'iyyar Patriotic Front mai mulkin kasa, ya lashe zaben da ya gudana a kwanakin baya da gagarumin rinjaye.
Uwar gida Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Zambia kasa ce dake da zumunta mai karfi da kasar Sin, kana tana cikin kasashen Afirka dake gudanar da hadin gwiwa tare da kasar Sin. Ta ce kasashen biyu suna goyowa juna baya tsahon lokaci, sun kuma samu nasarori da dama a fannoni daban daban.
Kaza lika Hua Chunying ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakaninta da Zambia, tare da fatan kara kwazo tare, domin inganta dangantakar hadin gwiwa a tsakaninsu.
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Edgar Lungu ya samu kuri'u da yawansu ya kai kashi 48.3 cikin dari, a babban zaben da ya gudana, zai kuma kasance shugaban kasar Zambia na shida, tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1964.
Tuni dai shugaba Lungu ya kafa sabuwar majalisar ministoci, mai kunshe da ministoci 22, ciki hadda 14 da za su yi tazarce. (Zainab)