in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga sabon shugaban Zambia
2015-01-31 17:02:50 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga sabon shugaban kasar Zambia Edgar Lungu.

Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce zumuncin gargajiya tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasar Zambia na ci gaba da kyautata, yayin da aka samu managarcin sakamako a fannin hadin gwiwar kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kara da cewa kasarsa na kara mai da hankali sosai game da bunkasar dangantakar abokantaka tsakaninta da Zambia, tana kuma fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwar kasashen yadda ya kamata, a wani mataki na kara inganta zaman rayuwar al'ummomin kasashen. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China