in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 290 sun rasu sakamakon hargitsin tsakanin sojoji da 'yan tawaye a Yemen
2014-07-09 10:22:57 cri

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa, akalla mutane 290 ne suka rasa rayukan a 'yan kwanakin nan, biyowa bayan kazamin dauki ba dadi da jami'an rundunar sojin kasar suka yi, da dakarun 'yan tawaye a lardunan Amran da Al-Jouf dake arewacin kasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar a ranar Talata ta ce, kimanin dakarun sojin kasar 50 ne suka rasu, baya ga mayakan 'yan Shi'a 240, yayin da kuma wasu mutanen da dama suka samu raunuka sakamakon fafatawar da bangarorin biyu suka yi. Hakan kuwa a cewar sanarwar, ya biyo bayan karyewar yarjejeniyar da aka cimma ne a baya.

Jaridun kasar ta Yamen dai sun buga hotunan wasu daga gawawwakin mutanen da rikicin ya ritsa da su a titunan birnin Amran, fadar mulkin lardin Amran, da kuma wadanda suka rasu a garuruwan al-Safra da Barakish dake lardin al-Jouf.

Tuni dai mahukuntan kasar suka kara yawan dakarun soji a yankunan shiga Amran, mai nisan kusan kilo mita 50 daga arewacin birnin Sanaa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China