in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kwashe wasu ma'aikatan ofishin jakadancinta dake Yemen saboda barazanar ta'addanci
2013-08-07 10:10:25 cri

Rundunar sojin sama ta kasar Amurka ta kwashe ma'aikata marasa muhimman ayyuka na ofishin jakadancinta dake Sanaa, babban birnin kasar Yemen, ranar Talata, bisa umarnin ma'aikatar harkokin waje, in ji hukumar tsaro ta Pentagon.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta yi gargadi a wannan rana da safe inda ta ba da odar kaurar ma'aikata marasa muhimman ayyuka daga Yemen, saboda ci gaban barazana na ta'addanci.

Ma'aikatar har wa yau ta gargadi 'yan kasar dangane da zuwa kasashen Larabawa, kana wadanda suke da zama a wadannan kasashe su fita daga cikinsu ba tare da bata lokaci ba, inda ta kara da cewa, barazana a fuskar tsaro a kasar Yemen na da girma matuka.

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta Pentagon, George Little ya baiyana cikin wata sanarwa cewa, hukumar kariya ta kasar Amurka za ta ci gaba da tabbatar da kasancewar jami'anta a kasar Yemen, domin taimakawa ma'aikatar harkokin wajen, da kuma sa ido kan harkokin tsaro.

Ita ma mai magana da yawun hukumar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, ta baiyana cikin wata sanarwa cewa, an damu matuka dangane da barazanar, dake nuna cewa, akwai alamun kai harin ta'addanci kan 'yan kasar Amurka da cibiyoyinta dake kasashen waje, musamman ma a yankunan kasashen Larabawa.

Don haka, aka dau matakan tabbatar da samar da kariya ga ma'aikata, har da 'yan wadannan kasashe dake aiki da su, da kuma wadanda suke kai ziyara a cibiyoyin kasar Amurka. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China