Akalla mutane 42 ne 'yan gudun hijira daga kasashen Afrika suka nutse a yammacin Lahadin nan 9 ga wata a gabar tekun Yemen bayan da jirgin da ke dauke da su ya kife a gabar ruwan Aden, an dai samu nasarar ceto mutane 30 daga cikin jirgin, in ji wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar tsaron Yemen.
Wannan hadarin dai ya auku ne a 'yan kilomita kadan daga gabar tekun Bir Ali na kudancin gundumar Shabwa dake kasar Yemen din da yammacin Lahadin, a cewar wannan sanarwa ta ma'aikatar tsaro a shafinta na yanar gizo.
Duk da cewar ma'aikatar tsaron ba ta kara wani haske a kan kasashen asali na wadannan mutane ba, amma mahukuntan yankin sun tabbatar da cewar, galibinsu daga Somaliya ne da Habasha.
Kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka bayyana daruruwan 'yan gudun hijira ne ke hallaka duk shekara a kokarin da suke yi na tsallakawa zuwa Yemen ta jiragen da suke wuce nauyin da zai iya dauka, a kokarin da suke na bi ta gabar tekun Aden da Baharmaliya domin su shiga kasashen Turai.
Fiye da mutane 62,000 ne masu neman mafaka, da 'yan gudun hijira da kuma 'yan ci rani suka isa Yemen daga kusurwar Afrika a shekarar bara kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta tabbatar. (Fatimah)