in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Yemen zai kafa gwamnatin hada kan kasa
2014-09-03 09:33:28 cri

Shugaban kasar Yemen Abd-Rabbu Mansour Hadi, ya bayyana aniyarsa ta maye gurbin gwamnatinsa da gwamnatin hada kan kasa, a wani kokari na kwantar da hankulan zanga-zangar baya-bayan nan da ta kunno kai a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Yemen Saba, ya bayar da rahoto a ranar Talata cewa, yanzu haka Hadi zai bayyana sabon firaministan kasar cikin mako guda wanda daga bisani zai kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar ta Yemen, shugaban kasa ne zai nada ministocin tsaro, harkokin cikin gida, kasashen waje, da kuma kudi wadanda za su kasance a cikin sabuwar gwamnati.

Shugaban ya kuma ce, gwamnatin za ta rage farashin mai ya zuwa kudin kasar riyals 25, kimanin dala 0.12 kan ko wace lita don faranta ran masu bore, sakamakon karin kudin mai da aka yi a watan Yuli.

Bugu da kari, shugaban ya bukaci shugabannin 'yan Shi'a da su janye mayakansu, daga ciki da wajen Sanaa, babban birnin kasar, su kuma janye daga lardin arewacin Amran, kana su tsagaita bude wuta kan sojoji da ke makwabtaka da lardin al-Jawf.

Sai dai kakakin mayakan Houthi 'yan Shi'a Mohammed Abdulsalam cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Internet, ya yi watsi da wannan kiran, yana mai cewa, ba za su yi watsi da al'amuran kasa da ke damun jama'arsu ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China