in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani bam da ya tashi cikin wata mota ya hallaka mutane 9 a Yemen
2013-06-03 10:47:13 cri

Rahotanni daga kasar Yemen sun tabbatar da mutuwar sojoji 9, sakamakon aukuwar wani harin bam da aka dasa shi cikin wata mota, a kusa da wani kamfanin sarrafa iskar gas na Balhaf, a lardin Shabwa dake kudu maso gabashin kasar.

Wani jami'in tsaron dake garin na Balhaf lokacin da lamarin ya auku, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, maharin da ake zargin 'dan kungiyar Al-Qaida ne, ya tada bam din ne dake cikin motar da yake tukawa a gaban ginin kamfanin sarrafa iskar gas din, sa'an nan kuma wasu gungun maharan dake cikin wata motar daban suka bude wuta ga jami'an tsaron dake wurin.

Tun da fari dai sai da wani jami'in ma'aikatar cikin gidan kasar ya bayyana wa Xinhua cewa, harin kunar bakin waken ya hallaka a kalla sojoji 5, tare da jikkata wasu da dama. Ko da yake dai bai yi karin bayani kan hakan ba. Shi dai wannan kamfanin sarrafa iskar gas na kasar Faransa, da aka bude shi a shekarar 2009, na karkashin kulawar kamfanin hada-hadar mai na Total, ya kuma sha fama da hare-haren kunar bakin wake, tun lokacin da zanga-zangar kin jinin gwamnatin tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh ta barke.

Kawo wannan lokaci, gwamnatin kasar na ci gaba da daukar matakan murkushe 'ya'yan kungiyar ta Al-Qaida a yankunan Shabwa, da kuma lardunan Abyan da Hadramout. Albarkatun mai ne ke daukar kaso 90 bisa dari na daukacin hajojin da kasar ta Yemen ke fitarwa waje.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China