A jiya Laraba shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin, ya ba da izini ga firaministan kasar Benjamin Netanyahu da ya kafa sabuwar gwamnatin kasar a hukunce.
Mr. Rivlin ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa da daren wannan rana, cewa bayan tattaunawarsa da jam'iyyu daban daban game da ayyukan kafa sabuwar gwamnatin kasar, ya yanke shawarar ba da izinin gudanar da wadannan aiki ga Netanyahu, wanda galibin jam'iyyu suka goyi baya.
Ya ce sabuwar gwamnatin za ta fuskanci kalubale uku, wato gyara hulda tsakaninta da babbar kawarta Amurka, da kawar da sabanin dake tsakanin jama'a game da babban zabe, da kuma kara neman amincewar jama'a ga tsayayyiyar gwamnati a kasar.
Izinin da Netanyahu ya samu na kafa sabuwar gwamnati, zai ba shi damar kammala wannan aiki cikin makwanni 4, da kuma karin makwanni 2 idan har akwai bukatar hakan.
An gudanar da zaben majalisar ministocin kasar Isra'ila ne a ranar 17 ga watan nan, inda jam'iyyar Likud mai sassaucin ra'ayi karkashin jagorancin Netanyahu ta lashe zaben, bayan ta doke kawancen farfado da Yahudawa.(Lami)