Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bukaci MDD da ta dauki matakai a game da hare-haren jiragen sama da kasar Isra'ila take kaiwa a kan wasu matsugunni 2 na sojojin Syria.
Wata majiya ta kamfanin dillancin labarai na Syria SANA, ta ce, ma'aikatar harkokin wajen Syria, a cikin wata takarda da ta rubutawa MDD ta ce, ya kamata a dau mataki kan Isra'ila, wacce bata boye manufofinta ba, kuma an gabatar da wannan takardar bayan awoyi kadan da wasu jiragen saman yaki na Isra'ila suka kai farmaki a wasu wurare biyu, ciki har da ofishin sojoji dake kusa da babban filin saukar jiragen sama na Damascus.
Ma'aikatar harkokin wajen ta ce, kamata ya yi a dauki duk matakan da suka dace domin haramtawa Isra'ila kara aiwatar irin wannan hari.
Tun farko kwamandan rundunar dakarun Syria ya ce, hare-haren da Isra'ilar ke kaiwa, yana nuni da hannun da Isra'ila take da shi wajen goyon bayan ta'addanci a Syria. (Suwaiba)