in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar ministocin Isra'ila ta amince da dokar kafa kasar Yahudawa
2014-11-24 12:07:48 cri

Majalisar ministocin Isra'ila ta amince da wani tsarin doka mai cike da takaddama, wanda ya amince a hukunce cewar kasar Isra'ila kasa ce mallakin Yahudaha.

An rattaba hannu kan doka duk kuwa da kasancewar ka ce na ce daga bangaren Labarawa da Yahudawa.

Ministoci 19 suka amince da dokar, kuma bakwai suka ki amincewa, daga cikin wadanda suka ki amincewa, har da ministan shari'a na kasar Tzipi Livni.

Kakakin firaminista Benjamin Netanyahou ya ce, duk da yake cewar an yi muhawarar ba tare da 'yan jarida ba, to amma wasu kafofi na watsa labarai sun ba da rahoto cewar, an yi musayar kalamai masu zafi tsakanin Livni da firaminista Netanyahu.

Dokar ta bayyana cewar, kasar Isra'ila kasa ce ta al'ummar Yahudawa, kuma hakan ya kasance 'yancin Yahudawa. Dokar ta kara jaddada cewar, harshen Hebrew shi ne yaren kasar, shi kuma harshen Larabci, an ba shi wani matsayi na musamman, dokar dai ta daga matsayin Yahudawa ta yadda ya zarce tsarin damokradiyya na kasar.

Ita dai sabuwar dokar ta zayyana cewar, za'a yi amfani da tsarin Yahudanci wajen fassara dokoki, watau a nan baza a yi amfani da na damokradiyya ba, kuma dokar ta ce, za ta yi aiki wajen samarwa Yahudawa 'yan kama wuri zamna wurin zama, to amma su 'yan kasar Larabawa dokar ba ta ce kome a kan su ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China