Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa game da yadda Isra'ila ke mamayar yankunan dake yamma da gabar kogin Jordan, matakin da a cewar sa ya yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa.
Tsokacin na Mr. Ban dai ya biyo bayan sanarwar da mahukunta a Isra'ilan suka fitar, game da fadada yankin kasar da wani fili mai fadin kusan eka 1,000 dake Bethlehem a yammacin gabar kogin na Jordan.
Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya kara da cewa, daukar irin wannan mataki na kwace filaye, na iya haifar da karin rigingimu da ake fatan kaucewa.
Sanarwar ta kuma rawaito babban magatakardar MDDr na kira ga Isra'ila, da ta amince da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke mata, game da dakatar da mamayar wurare ba bisa ka'ida ba, ta kuma rungumu ka'idojin kasa da kasa masu alaka da hakan. (Saminu)