in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta amince da gina karin matsugunan Yahudawa a gabashin birnin Kudus
2014-12-25 10:07:15 cri

Mahukunta a birnin Kudus sun amince da ginin sabbin matsugunan Yahudawa kimanin 400, a wasu filaye da Isra'ila ta kwace yayin yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967.

Rahotanni sun bayyaana cewa, kwamitin tsara gine-gine na birnin Kudus din ya amince da gina gidaje 380 a wannan yanki, da suka hada da gidaje 307 a arewa maso gabashin Ramot, da kuma gidaje 73 a Har Homa.

Wani jami'in gwamnatin birnin na Kudus Pepe Alalu, ya bayyana wa manema labaru cewa, dukkanin wani yunkuri na dinke baraka, tare da cimma matsayar amincewa juna a yankin ta faskara, don haka Isra'ila ta amince da gina wadannan gidaje domin al'ummar Yahudawa.

Tun cikin watan Oktobar da ya gabata ne mahukuntan Isra'ila suka bayyana shirin ginin gidaje 2,600 a yankunan dake kusa da Givat Hamtos, matakin da Amurka ta yi matukar suka, ya kuma kara fadada banbancin dake tsakanin Amurkan da Isra'ila. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China